We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

Nehemiya 7

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← Nehemiya 6 Nehemiya Nehemiya 8 →

1Bayan an sāke gina katangar na kuma sa ƙofofi a wurarensu, sai aka naɗa masu tsaro, da mawaƙa, da Lawiyawa.

2Na sa ɗan’uwana Hanani tare da Hananiya shugaban fada aikin riƙon Urushalima, domin shi Hananiya mutum mai mutunci ne, mai tsoron Allah fiye da yawancin mutane.

3Na ce musu, “Kada a buɗe ƙofofin Urushalima da sassafe sai rana ta fito sosai. Yayinda matsaran ƙofofi suna aiki, a kulle ƙofofin a sa musu sakata kafin matsaran su tashi, wajen fāɗuwar rana. Ku kuma naɗa mazaunan Urushalima a matsayin masu tsaro, waɗansunsu a wuraren aiki, waɗansun kuma kusa da gidajensu.”

4Birnin Urushalima kuwa tana da fāɗi da girma, amma mutanen da suke zama a cikinta kaɗan ne, ba a kuma gina gidaje da yawa ba tukuna.

5Sai Allahna ya sa a zuciyata in tara manyan gari, shugabanni da talakawa don a rubuta su bisa ga iyalansu. Na sami littafin asali na waɗanda suka fara dawowa. Ga abin da na tarar an rubuta a ciki.

6Waɗannan su ne mutanen yankin da suka dawo daga zaman bautar da Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kame (sun dawo Urushalima da Yahuda, kowanne zuwa garinsa.

7Sun dawo tare da Zerubbabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Azariya, da Ra’amiya, da Nahamani, da Mordekai, da Bilshan, da Misfar, da Bigwai, da Nehum da kuma Ba’ana).

8Zuriyar

9ta Shefatiya 372

10ta Ara 652

11ta Fahat-Mowab (ta wurin Yeshuwa da Yowab) 2,818

12ta Elam 1,254

13ta Zattu 845

14ta Zakkai 760

15ta Binnuyi 648

16ta Bebai 628

17ta Azgad 2,322

18ta Adonikam 667

19ta Bigwai 2,067

20ta Adin 655

21ta Ater (ta wurin Hezekiya) 98

22ta Hashum 328

23ta Bezai 324

24ta Harif 112

25ta Gibeyon 95.

26Mutanen

27na Anatot 128

28na Bet-Azmawet 42

29na Kiriyat Yeyarim, Kefira da na Beyerot 743

30na Rama da na Geba 621

31na Mikmash 122

32na Betel da na Ai 123

33na ɗayan Nebo 52

34na ɗayan Elam 1,254

35na Harim 2 320

36na Yeriko 345

37na Lod, da na Hadid, da na Ono 721

38na Sena’a 3,930.

39Ga zuriyar Firistoci.

40ta Immer 1,052

41ta Fashhur 1,247

42ta Harim 1,017.

43Ga zuriyar Lawiyawa.

44Mawaƙa.

45Ga zuriyar Matsaran Ƙofofi.

46Ma’aikatan haikali.

47da ta Keros, da ta Siya, da ta Fadon,

48da ta Lebana, da ta Hagaba, da ta Shalmai,

49da ta Hanan, da ta Giddel, da ta Gahar,

50da ta Reyahiya, da ta Rezin, da ta Nekoda,

51da ta Gazzam, da ta Uzza, da ta Faseya,

52da ta Besai, da ta Meyunawa, da ta Nefussiyawa,

53da ta Bakbuk, da ta Hakufa, da ta Harhur,

54da ta Bazlit, da ta Mehida, da ta Harsha,

55da ta Barkos, da ta Sisera, da ta Tema,

56da ta Neziya, da kuma ta Hatifa.

57Ga zuriyar bayin Solomon.

58da ta Ya’ala, da ta Darkon, da ta Giddel,

59Shefatiya, Hattil,

60Zuriyar ma’aikatan haikali da ta bayin Solomon su 392.

61Waɗansu sun hauro daga garuruwan Tel-Mela, Tel-Harsha, Kerub, Addon da Immer, amma ba su iya nuna cewa iyalansu su zuriyar Isra’ila ce ba,

62zuriyar

63Na wajen firistoci kuwa su ne,

64Waɗannan ne aka nemi sunayensu a cikin tarihin asalin iyalai, amma ba a same su a ciki ba, saboda haka aka hana su shiga cikin firistoci, sun zama kamar marasa tsarki.

65Sai gwamna ya umarce su kada su ci wani abinci mafi tsarki, sai akwai firist da zai nemi nufin Ubangiji ta wurin Urim da Tummim.

66Yawan jama’ar duka ya kai mutum 42,360,

67ban da bayinsu maza da mata 7,337. Suna kuma da mawaƙa maza da mata 245.

68Akwai dawakai 736, alfadarai 245

69raƙuma 435, da kuma jakuna 6,720.

70Waɗansu shugabannin iyalai suka ba da kyautai domin taimakon aiki. Gwamna ya ba da darik 1,000 na zinariya, kwanoni 50, da riguna 530 don firistoci.

71Waɗansu shugabannin iyalai sun ba da darik 20,000 na zinariya da mina 2,200 na azurfa don aiki.

72Jimillar da sauran mutane suka bayar ta kai darik 20,000 na zinariya, minas 2,000 na azurfa, da riguna sittin da bakwai don firistoci.

73Firistoci, da Lawiyawa, da matsaran ƙofofi, da mawaƙa, da ma’aikatan haikali tare da waɗansu mutane da kuma sauran mutanen Isra’ila, suka zauna a garuruwansu.

← Nehemiya 6 Nehemiya Nehemiya 8 →