1To, fa, shugabannin mutane suka zauna a Urushalima, sauran mutanen kuma suka jefa ƙuri’a don su kawo mutum ɗaya daga kowane mutum goma don su zauna a Urushalima, birni mai tsarki, yayinda sauran tara suka zauna a garuruwansu.
2Sai mutane suka yaba wa dukan mutanen da suka ba da kansu da yardar rai su zauna a Urushalima.
3Waɗannan su ne shugabannin yankuna waɗanda suka zauna a Urushalima (ko da yake waɗansu Isra’ilawa, da firistoci, da Lawiyawa, da ma’aikatan haikali, da zuriyar bayin Solomon, suka yi zama a cikin garuruwan Yahuda, kowanne a mallakarsa cikin garuruwa dabam-dabam,
4yayinda sauran mutane daga Yahuda da Benyamin suka zauna a Urushalima).
5da Ma’asehiya ɗan Baruk, ɗan Kol-Hoze, ɗan Hazahiya, ɗan Adahiya, ɗan Yohiyarib, ɗan Zakariya, zuriyar Shela.
6Zuriyar Ferez waɗanda suka zauna a Urushalima sun kai ɗari huɗu da sittin da takwas, dukansu kuwa muhimman mutane ne.
7Daga zuriyar Benyamin akwai,
8da mabiyansa, Gabbai da Sallai, mutum 928.
9Yowel ɗan Zikri ne babban shugabansu, Yahuda kuma ɗan Hassenuwa, ya shugabanci Yanki na Biyu na birni.
10Daga firistoci akwai,
11da Serahiya ɗan Hilkiya, ɗan Meshullam, ɗan Zadok, ɗan Merahiyot, ɗan Ahitub, mai lura da abubuwa a cikin gidan Allah,
12tare da ’yan’uwansu waɗanda suke aiki domin haikali, su 822 ne.
13da ’yan’uwansa waɗanda suke shugabannin iyalai, su 242.
14da ’yan’uwansa, su 128 ne muhimman mutane.
15Daga Lawiyawa kuwa akwai,
16da Shabbetai, da kuma Yozabad, biyu cikin shugabanni Lawiyawa waɗanda suke da nawayar aiki waje da gidan Allah.
17Sai kuma Mattaniya ɗan Mika, ɗan Zabdi, ɗan Asaf, shugaban da yake bi da hidimar godiya da kuma addu’a.
18Lawiyawan da suke cikin birni mai tsarki sun kai 284.
19Matsaran ƙofofi kuwa su ne,
20Sauran Isra’ilawa tare da firistoci, da Lawiyawa sun kasance a dukan garuruwan Yahuda, kowanne a mallakar kakansa.
21Ma’aikatan haikali sun zauna a kan tudun Ofel. Ziha, da Gishfa ne suke lura da su.
22Babban shugaban Lawiyawa a Urushalima shi ne Uzzi ɗan Bani, ɗan Hashabiya, ɗan Mattaniya, ɗan Mika. Uzzi yana ɗaya daga zuriyar Asaf, waɗanda suke mawaƙan da suke da nawayar hidima a gidan Allah.
23Mawaƙa sun bi umarnan sarki, a kan abin da za su yi kowace rana.
24Fetahahiya ɗan Meshezabel, ɗaya daga zuriyar Zera ɗan Yahuda ne, wakilin sarki cikin dukan al’amuran da suka shafi mutane.
25Game da ƙauyukan da filayensu, waɗansu mutanen Yahuda suka zauna a Kiriyat Arba da ƙauyukanta, da Dibon da ƙauyukanta, da Yekabzeyel da ƙauyukanta.
26Akwai su kuma a Yeshuwa, da Molada, da Bet-Felet,
27da Hazar Shuwal, da Beyersheba da ƙauyukanta.
28Akwai su a Ziklag, da Mekona da ƙauyukanta.
29Suna nan kuma a En Rimmon, da Zora, da Yarmut,
30da Zanowa, da Adullam da ƙauyukansu, da Lakish da gonakinta, da kuma Azeka da ƙauyukanta. Saboda haka sun yi zama tun daga Beyersheba har zuwa Kwarin Hinnom.
31Zuriyar mutanen Benyamin daga Geba sun zauna a Mikmash, da Aiya, da Betel da ƙauyukanta,
32da Anatot, da Nob, da Ananiya,
33da Hazor, da Rama, da Gittayim,
34da Hadid, da Zeboyim, da Neballat,
35da Lod, da Ono, da kuma a Kwarin Masu sana’a.
36Waɗansu gundumomin Lawiyawan Yahuda sun zauna a Benyamin.