We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

Farawa 49

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← Farawa 48 Farawa Farawa 50 →

1Sai Yaƙub ya kira ’ya’yansa maza ya ce, “Ku tattaru don in faɗa muku abin da zai faru gare ku, a kwanaki masu zuwa.

2“Ku tattaru, ku saurara, ’ya’yan Yaƙub maza;

3“Ruben, kai ne ɗan farina,

4Mai tumbatsa kamar ruwa, amma ba za ka ƙara zama mai daraja ba,

5“Simeyon da Lawi ’yan’uwa ne,

6Ba zan shiga shawararsu ba,

7La’ananne ne fushinsu, mai tsanani ne ƙwarai,

8“Yahuda,49.8 Yahuda ya yi kamar ya fito daga Ibraniyanci na yabo ne. ’yan’uwanka za su yabe ka;

9Kai ɗan zaki ne, ya Yahuda,

10Kursiyi ba zai tashi daga Yahuda ba,

11Zai daure jakinsa a kuringa,

12Idanunsa za su duhunce fiye da ruwan inabi,

13“Zebulun zai zauna a bakin teku,

14“Issakar doki49.14 Ko kuwa mai ƙarfi mai ƙarfi,

15Sa’ad da ya ga yadda wurin hutunsa yana da kyau

16“Dan49.16 Dan a nan yana nufin yakan tanada adalci. zai tanada adalci wa mutanensa

17Dan zai zama maciji a gefen hanya,

18“Ina zuba ido ga cetonka, ya Ubangiji.

19“Masu fashi za su fāɗa wa Gad,49.19 Gad na iya nufin fāɗawa da kuma ƙungiyar mahara.

20“Abincin Asher zai zama a wadace,

21“Naftali sakakkiyar barewa ce

22“Yusuf kuringa ce mai ba da amfani.

23Da ɗaci rai mahara suka fāɗa masa;

24Amma bakansa yana nan daram

25saboda Allah na mahaifinka, wanda ya taimake ka,

26Albarkun mahaifi suna da girma fiye

27“Benyamin kyarkeci ne mai kisa;

28Dukan waɗannan su ne kabilu goma sha biyu na Isra’ila, kuma abin da mahaifinsu ya faɗa musu ke nan sa’ad da ya albarkace su, yana ba kowane albarkar da ta dace da shi.

29Sa’an nan ya ba su waɗannan umarnai ya ce, “Ina gab da a tara ni ga mutanena. Ku binne ni tare da kakannina a kogon da yake cikin filin Efron mutumin Hitti,

30kogon da yake cikin filin Makfela, kusa da Mamre a Kan’ana, wanda Ibrahim ya saya tare da filin, yă zama makabarta daga Efron mutumin Hitti.

31A can aka binne Ibrahim da matarsa Saratu, a can aka binne Ishaku da matarsa Rebeka, a can kuma na binne Liyatu.

32Filin tare da kogon da yake ciki, an saya daga Hittiyawa.”49.32 Ko kuwa ’ya’ya mazan Het

33Sa’ad da Yaƙub ya gama ba da umarnan ga ’ya’yansa maza, sai ya ɗaga ƙafafunsa zuwa gado, ya ja numfashinsa na ƙarshe, aka kuwa tara shi ga mutanensa.

← Farawa 48 Farawa Farawa 50 →