We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

Farawa 36

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← Farawa 35 Farawa Farawa 37 →

1Waɗannan su ne zuriyar Isuwa (wato, Edom).

2Isuwa ya ɗauko matansa daga cikin matan Kan’ana, ya ɗauko Ada ’yar Elon mutumin Hitti, da Oholibama ’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon Bahiwiye

3ya kuma auri Basemat ’yar Ishmayel wadda take ’yar’uwar Nebayiwot.

4Ada ta haifi wa Isuwa, Elifaz. Basemat kuma ta haifa masa Reyuwel.

5Oholibama kuwa ta haifa masa Yewush, Yalam da Kora. Waɗannan su ne ’ya’yan Isuwa maza, waɗanda aka haifa masa a Kan’ana.

6Isuwa ya ɗauki matansa da ’ya’yansa maza da mata da kuma dukan membobin gidansa, ya kuma ɗauki shanunsa da dukan sauran dabbobinsa, da dukan dukiyarsa da ya samu a ƙasar Kan’ana zuwa wata ƙasa nesa da ɗan’uwansa Yaƙub.

7Mallakarsu ta yi yawa ƙwarai da ba za su iya zauna tare ba; gama ƙasar da suke zaune a ciki ba za tă ishe su su biyu ba saboda dabbobinsu.

8Saboda haka Isuwa (wato, Edom) ya zauna a ƙasar tuddai na Seyir.

9Wannan shi ne zuriyar Isuwa, kakan mutanen Edom, a ƙasar tuddai na Seyir.

10Waɗannan su ne sunayen ’ya’yan Isuwa maza,

11’Ya’yan Elifaz maza su ne,

12Elifaz ɗan Isuwa kuma yana da ƙwarƙwara mai suna Timna, wadda ta haifa masa Amalek. Waɗannan su ne jikokin Ada matar Isuwa.

13’Ya’yan Reyuwel maza su ne,

14’Ya’yan Oholibama maza ’yar Ana wadda take jikanyar Zibeyon, matar Isuwa, waɗanda ta haifa wa Isuwa su ne,

15Waɗannan su ne manya a cikin zuriyar Isuwa,

16Kora,36.16 Masoretik, Fentatut na Samariya (dubi kuma Far 36.11 da 2Tar 1.3-6) ba su da Kora. Gatam da kuma Amalek. Waɗannan ne manya da suka fito daga dangin Elifaz a Edom; su ne jikokin Ada.

17’Ya’yan Reyuwel maza,

18’Ya’yan Oholibama maza matar Isuwa,

19Waɗannan su ne ’ya’yan Isuwa maza (wato, Edom), waɗannan ne manyansu.

20Waɗannan su ne ’ya’yan Seyir Bahore maza, waɗanda suke zaune a yankin,

21Dishon, Ezer da Dishan. Waɗannan su ne manyan Horiyawa, ’ya’yan Seyir, maza, a ƙasar Edom.

22’Ya’yan Lotan maza su ne,

23’Ya’yan Shobal maza su ne,

24’Ya’yan Zibeyon maza su ne,

25’Ya’yan Ana su ne,

26’Ya’yan Dishon maza36.26 Da Ibraniyanci Dishan, wani suna na Dishon su ne,

27’Ya’yan Ezer maza su ne,

28’Ya’yan Dishan maza su ne,

29Waɗannan su ne manyan Horiyawa,

30Dishon, Ezer da Dishan.

31Waɗannan su ne sarakunan da suka yi mulki a Edom kafin wani sarki mutumin Isra’ila yă yi mulki,36.31 Ko kuwa kafin wani sarkin Isra’ilawa ya yi mulki a kansu

32Bela ɗan Beyor ya zama sarkin Edom. Sunan birninsa shi ne Dinhaba.

33Sa’ad da Bela ya rasu, Yobab ɗan Zera daga Bozra ya gāje shi.

34Sa’ad da Yobab ya rasu, Husham daga ƙasar Temaniyawa ya gāje shi.

35Sa’ad da Husham ya rasu, Hadad ɗan Bedad, wanda ya ci Midiyan da yaƙi a ƙasar Mowab, ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Awit.

36Sa’ad da Hadad ya rasu, Samla daga Masreka ya gāje shi.

37Sa’ad da Samla ya rasu, Sha’ul daga Rehobot na ta kogi36.37 Mai yiwuwa Yuferites ya gāje shi.

38Sa’ad da Sha’ul ya rasu, Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya gāje shi.

39Sa’ad da Ba’al-Hanan ɗan Akbor ya rasu, Hadad36.39 Yawancin rubuce-rubucen hannu na Masoretik, Fentatut na Samariya da Siriyak (dubi kuma 1Tar 1.50); yawancin rubuce-rubucen hannu na Masoretik suna da Hadar ne. ya gāje shi. Sunan birninsa shi ne Fau, kuma sunan matarsa Mehetabel ce ’yar Matired, jikanyar Me-Zahab.

40Waɗannan su ne manya da suka fito daga zuriyar Isuwa, bisa ga danginsu, bisa kuma ga kabilansu da yankunansu. Sunayensu su ne,

41Oholibama, Ela, Finon.

42Kenaz, Teman, Mibzar.

43Magdiyel da Iram.

← Farawa 35 Farawa Farawa 37 →