We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

Farawa 16

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← Farawa 15 Farawa Farawa 17 →

1To, Saira, matar Abram, ba tă haifa masa ’ya’ya ba. Amma tana da wata baiwa mutuniyar Masar mai suna Hagar,

2saboda haka sai ta ce wa Abram, “Ubangiji ya hana mini haihuwar ’ya’ya. Tafi ka kwana da baiwata; wataƙila in sami iyali ta wurinta.”

3Saboda haka bayan Abram ya yi zama a Kan’ana shekaru goma, Saira matarsa ta ɗauki Hagar baiwarta ta ba wa mijinta tă zama matarsa.

4Abram kuwa ya kwana da Hagar, ta kuma yi ciki.

5Sai Saira ta ce wa Abram, “Kai ne da alhakin wahalan nan da nake sha. Na sa baiwata a hannunka, yanzu da ta sani tana da ciki, sai ta fara rena ni. Bari Ubangiji yă shari’anta tsakanina da kai.”

6Abram ya ce, “Baiwarki tana a hannunki? Ki yi da ita yadda kika ga ya fi kyau.” Sai Saira ta wulaƙanta Hagar; saboda haka ta gudu daga gare ta.

7Mala’ikan Ubangiji ya sami Hagar kusa da maɓulɓula a jeji, ita ce maɓulɓular da take gefen hanya zuwa Shur.

8Ya kuma ce mata, “Hagar, baiwar Saira, daga ina kika fito, kuma ina za ki?”

9Sai mala’ikan Ubangiji ya ce mata, “Koma wurin uwargijiyarki Saira, ki yi mata biyayya.”

10Mala’ikan ya ƙara da cewa, “Zan ƙara zuriyarki har su yi yawan da ba wanda zai iya lasafta su.”

11Mala’ikan Ubangiji ya kuma ce mata,

12Zai zama mutum mai halin jakin jeji.

13Sai ta ba wa Ubangiji wanda ya yi magana da ita, wannan suna. “Kai Allah ne wanda yake ganina,” gama ta ce, “Yanzu na ga wanda yake ganina.”

14Shi ya sa ake kira rijiyar Beyer-Lahai-Royi16.14 Beyer-Lahai-Royi yana nufin rijiyar Mai Rai wanda yake ganina. tana nan har yanzu, tsakanin Kadesh da Bered.

15Haka fa Hagar ta haifa wa Abram ɗa, Abram kuwa ya ba da suna Ishmayel ga ɗan da ta haifa.

16Abram yana da shekaru 86 sa’ad da Hagar ta haifa masa Ishmayel.

← Farawa 15 Farawa Farawa 17 →