1Wannan shi ne labarin Shem, Ham da Yafet, ’ya’yan Nuhu maza, waɗanda su ma sun haifi ’ya’ya maza bayan ambaliyar.
2’Ya’yan10.2 ’Ya’ya maza na iya nufin zuriyoyi Ko kuwa magāda ko al’ummai; haka ma a ayoyi 3, 4, 6, 7, 20-23, 29 da 31. Yafet maza su ne,
3’Ya’yan Gomer maza su ne,
4’Ya’yan maza Yaban su ne,
5(Daga waɗannan mutane ne masu zama a bakin teku suka bazu zuwa cikin ƙasashensu da kuma cikin al’ummansu, kowanne da yarensa.)
6’Ya’yan Ham maza su ne,
7’Ya’yan Kush maza su ne,
8Kush shi ne mahaifin Nimrod wanda ya yi girma ya zama jarumin yaƙi a duniya.
9Shi babban maharbi ne a gaban Ubangiji. Shi ya sa akan ce, kamar Nimrod babban maharbi a gaban Ubangiji.
10Cibiyoyin mulkinsa na farko su ne Babilon, Erek, Akkad, da Kalne a cikin Shinar.
11Daga wannan ƙasa, sai ya tafi Assuriya, inda ya gina Ninebe, Rehobot Ir, Kala
12da Resen, wadda take tsakanin Ninebe da Kala; wanda yake babban birni.
13Mizrayim shi ne mahaifin
14Fetrusiyawa, da Kasluhiyawa (inda Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftorawa.
15Kan’ana shi ne mahaifin,
16Yebusiyawa, Amoriyawa, Girgashiyawa,
17Hiwiyawa, Arkiyawa, Siniyawa,
18Arbadiyawa, Zemarawa, da Hamawa.
19har iyakar Kan’ana ta kai Sidon ta wajen Gerar har zuwa Gaza, sa’an nan ta milla zuwa Sodom, Gomorra, Adma da Zeboyim, har zuwa Lasha.
20Waɗannan su ne ’ya’yan Ham maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.
21Aka kuma haifa wa Shem, wan Yafet, ’ya’ya maza. Shem shi ne kakan ’ya’yan Eber duka.
22’Ya’yan Shem maza su ne,
23’Ya’yan Aram maza su ne,
24Arfakshad ne mahaifin10.24 Da Ibraniyanci; Seftuwajin, mahaifin shi ne Kainan, Kainan kuwa shi ne mahaifin Shela.
25Aka haifa wa Eber ’ya’ya maza biyu.
26Yoktan shi ne mahaifin,
27Hadoram, Uzal, Dikla,
28Obal, Abimayel, Sheba,
29Ofir, Hawila da Yobab. Dukan waɗannan ’ya’yan Yoktan maza ne.
30Yankin da suka zauna ya miƙe daga Mesha zuwa wajen Sefar a gabashin ƙasar tudu.
31Waɗannan su ne ’ya’yan Shem maza bisa ga zuriyarsu da yarurrukansu, cikin ƙasashensu da kuma al’ummominsu.
32Waɗannan su ne zuriyar ’ya’yan Nuhu maza bisa ga jerin zuriyarsu cikin al’ummominsu. Daga waɗannan ne al’ummomi suka bazu ko’ina a duniya bayan ambaliya.