1Maganar Ubangiji ta zo gare ni cewa,
2“Ɗan mutum, ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yake cewa wa ƙasar Isra’ila,
3Ƙarshe yanzu yana a kanki.
4Ba zan dube ki da tausayi;
5“Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,
6Ƙarshe ya zo!
7Ƙaddara ta auko miki,
8Ina gab da fasa hasalata a kanki
9Ba zan dube ki da tausayi
10“ ‘Ga shi ranar ta zo!
11Rikici ya yi girma ya zama
12Lokaci ya yi!
13Mai sayarwa ba zai mayar da ƙasar da ya sayar tuntuni ba
14“ ‘Ko da yake suna busa ƙaho suna kuma shirya kome,
15A waje takobi ne,
16Duk waɗanda suka tsira suka tsere za su kasance a cikin duwatsu,
17Kowane hannu zai raunana,
18Za su sa tufafin makoki su kuma rufu da fargaba.
19“ ‘Za su zubar da azurfarsu a tituna,
20Sun yi fariya kyan kayan adonsu
21Zan ba da su duka kamar ganima ga baƙi
22Zan juye fuskata daga gare su,
23“ ‘Ka shirya sarƙoƙi,
24Zan kawo al’ummai mafi mugunta su mallaki gidajenku;
25Sa’ad da wahala ta zo,
26Masifa a kan masifa za su zo,
27Sarki zai yi makoki, yerima zai fid da zuciya,