1Sa’an nan Musa da Isra’ilawa suka rera wannan waƙa ga Ubangiji suka ce,
2“Ubangiji ne ƙarfina da mafakata,
3Ubangiji mai yaƙi ne
4Karusan Fir’auna da sojojinsa
5Zurfafan ruwaye sun rufe su;
6Hannun damanka, ya Ubangiji,
7“A cikin girman kwarjininka
8Da hucin numfashin hancinka
9Magabci ya yi fahariya, cewa
10Amma ka hura numfashinka
11Wane ne cikin alloli,
12“Ka miƙa hannunka na dama,
13A cikin ƙaunarka marar iyaka, za ka bishe
14Al’ummai za su ji, su yi rawar jiki
15Sarakunan Edom za su tsorata,
16Razana da tsoro za su fāɗo a kansu.
17Za ka kawo su, ka dasa su
18“Ubangiji zai yi mulki
19Sa’ad da dawakai, kekunan yaƙi da mahayan dawakan Fir’auna suka shiga cikin teku, Ubangiji ya mayar da ruwan teku a kansu, amma Isra’ilawa suka wuce a cikin teku a busasshiyar ƙasa.
20Sa’an nan Miriyam annabiya, ’yar’uwar Haruna ta ɗauki ganga a hannunta, dukan mata kuwa suka bi ta, da ganguna suna rawa.
21Miriyam ta yi musu waƙa.
22Sai Musa ya jagoranci Isra’ila daga jan teku zuwa hamadar Shur. Kwana uku suka yi tafiya cikin hamada ba su sami ruwa ba.
23Da suka zo Mara, ba su iya shan ruwan ba saboda yana da ɗaci (shi ya sa ake kira wurin Mara).
24Sai mutanen suka yi gunaguni a kan Musa, suna cewa, “Me za mu sha?”
25Sai Musa ya yi kuka ga Ubangiji, Ubangiji kuwa ya nuna masa wani itace. Sai ya jefa shi cikin ruwan, sai ruwan ya zama mai daɗi.
26Ya ce, “In kun kasa kunne ga muryar Ubangiji Allahnku kuka yi abin da yake daidai a idanunsa, in kun mai da hankali ga umarnansa, kuka kiyaye dukan farillansa, ba zan kawo muku wani ciwon da na kawo a kan Masarawa ba, gama ni ne Ubangiji da nake warkar da ku.”
27Sai suka zo Elim inda akwai maɓulɓulan ruwa goma sha biyu da itatuwan dabino saba’in, suka sauka a can, kusa da ruwa.