We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

Esta 7

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← Esta 6 Esta Esta 8 →

1Saboda haka sarki da Haman suka tafi cin abinci wurin sarauniya Esta.

2Yayinda suke shan ruwan inabi a rana ta biyun nan, sai sarki ya sāke tambaya, “Sarauniya Esta, me kike so? Za a ba ki. Mene ne roƙonki? Ko da rabin masarautata ne, za a ba ki.”

3Sai Sarauniya Esta ta amsa ta ce, “In na sami tagomashi a wurinka, ya sarki, in kuma mai girma ya yarda, a bar ni da raina, wannan shi ne roƙona. Ka kuma sa kada a kashe mutanena, wannan ita ce bukata.

4Gama an sayar da ni da mutanena don a hallaka, a karkashe mu, a kuma ƙi mu. Da a ce an sayar da mu kamar bayi maza da mata ne, da na yi shiru, domin wannan zai zama abin da bai taka kara ya karye ba, har da za a dami sarki a kai.”7.4 Ko kuwa tabbatacce, gama ladar da abokin gābanmu zai bayar ba za a kwatanta da hasarar da sarki zai yi ba

5Sarki Zerzes ya tambayi Sarauniya Esta ya ce, “Wane ne shi? Ina mutumin da ya yi ƙarfin halin yin wannan karambani?”

6Esta ta ce, “Maƙiyi da abokin gāban, shi ne wannan mugun Haman.”

7Sarki ya tashi cikin fushi, ya bar ruwan inabinsa, ya fita zuwa cikin lambun fada. Amma da Haman ya gane cewa sarki ya riga ya yanke shawara a kan ƙaddararsa, ya dakata domin yă roƙi sarauniya Esta saboda ransa.

8Sarki yana dawowa daga lambun fada zuwa babban zauren liyafan ke nan, sai ga Haman ya fāɗi a kan shimfiɗar da Esta take zaune.

9Sai Harbona, ɗaya daga cikin bābānni masu yi wa sarki hidima ya ce, “Akwai wurin rataye mai laifi da tsayinsa ya kai ƙafa saba’in da biyar7.9 Da Ibraniyanci kamu hamsin (wajen mita 23). yana nan tsaye kusa da gidan Haman. Ya gyara shi ne domin a rataye Mordekai, wanda ya yi cece sarki wanda ya tone makircin masu niyya su hallaka sarki.”

10Saboda haka suka rataye Haman a kan wurin rataye mai laifin da shi Haman ya shirya saboda Mordekai. Sa’an nan sarki ya huce.

← Esta 6 Esta Esta 8 →