We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

Ezra 8

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← Ezra 7 Ezra Ezra 9 →

1Waɗannan su ne shugabannin iyalai, da kuma waɗanda suka dawo tare da ni daga Babilon a zamanin mulkin Sarki Artazerzes.

2Daga zuriyar Finehas,

3ɗan zuriyar Shekaniya ne shugaba,

4daga Fahat-Mowab,

5daga zuriyar Zattu,

6daga zuriyar Adin,

7daga zuriyar Elam,

8daga zuriyar Shefatiya,

9daga iyalin Yowab,

10daga Bani,

11daga Bebai,

12daga iyalin Azgad,

13zuriya ta Adonikam ne suka zo daga ƙarshe,

14daga zuriyar Bigwai,

15Na kuma tattara su a bakin rafi wanda yake gangarawa zuwa Ahawa, muka kafa sansani a can kwana uku. Da na bincika cikin mutane da firistoci, sai na tarar babu Lawiyawa.

16Saboda haka sai na aika a kira Eliyezer, da Ariyel, da Shemahiya, da Elnatan, da Yarib, da Natan, da Zakariya, da Meshullam waɗanda su ne shugabanni. Na kuma sa a kira Yohiyarib da Elnatan waɗanda masana ne.

17Na sa su je wurin Iddo wanda yake shugaba a Kasifiya. Aka gaya musu abin da za su gaya wa Iddo da ’yan’uwansa masu aiki a haikali a Kasifiya don su aiko mana waɗanda za su yi mana hidima a haikalin Allahnmu.

18Da yake Allah yana tare da mu, sai suka aiko mana da Sherebiya, wanda ya iya aiki, shi daga zuriyar Mali ɗan Lawi ne, ɗan Isra’ila. Sai ya zo tare da ’ya’yansa da kuma ’yan’uwansa. Dukansu dai mutum 18 ne.

19Suka kuma aika da Hashabiya tare da Yeshahiya daga zuriyar Merari, da ’yan’uwansu da kuma ’ya’yansu, su kuma mutum 20 ne.

20Sun kuma kawo masu aiki a haikali mutum 220, ƙungiyar da Dawuda da abokan aikinsa suka keɓe don su taimaki Lawiyawa aiki. Duk aka rubuta waɗannan da sunayensu.

21A can, a bakin rafin Ahawa, na sa mu yi azumi, domin mu ƙasƙantar da kanmu a gaban Allah, mu kuma roƙe shi yă kiyaye mana hanya, da mu da ’ya’yanmu da kayanmu duka.

22Na ji kunya in roƙi sarki yă haɗa mu da sojoji da masu dawakai don su yi mana rakiya su kāre mu daga magabta a kan hanya, gama mun ce wa sarki, “Alherin Allah yana tare da duk wanda yake dogara gare shi, amma kuma fushinsa yana kan duk wanda ya juya masa baya.”

23Saboda haka sai muka yi azumi, muka kai roƙonmu a wurin Allah, ya kuwa amsa mana.

24Sai na keɓe manyan firistoci guda goma sha biyu tare da Sherebiya, Hashabiya da kuma ’yan’uwansu guda goma.

25Na auna musu zinariya da azurfa, da kwanoni waɗanda sarki da mashawartansa, da sauran abokan aikinsa, da Isra’ilawan da suke can suka bayar domin haikalin Allahnmu.

26Na auna musu talenti 650 na azurfa, talenti ɗari na kwanonin azurfa, talenti 100 na zinariya,

27kwanonin zinariya guda 20 da darajarsu ya kai darik 1,000, da kwanoni biyu na gogaggen tagulla, wanda yake darajarsa daidai da zinariya.

28Na ce masa, “Ku da kayan nan tsarkaka ne ga Ubangiji. Azurfa da zinariya ɗin, bayarwa ce ta yardar rai ga Ubangiji, Allah na kakanninku.

29Ku lura da su da kyau har sai kun isa Urushalima. Ku auna su a shirayin haikalin Ubangiji a Urushalima, a gaban manyan firistoci, da Lawiyawa, da shugabannin iyalai na Isra’ila.”

30Sa’an nan sai firistoci, da Lawiyawa suka karɓi azurfa da zinariya da kuma tsarkakan kwanonin da aka auna don a kai haikalin Allahnmu a Urushalima.

31A rana ta goma sha biyu ga watan farko, muka tashi daga bakin rafin Ahawa don mu tafi Urushalima. Alherin Allahnmu yana tare da mu, ya kuma kāre mu daga magabta da ’yan fashi.

32Muka iso Urushalima, inda muka huta kwana uku.

33A rana ta huɗu muka tafi haikalin Allah, muka auna azurfa, da zinariya, da tsarkakan kwanonin, muka ba Meremot ɗan Uriya firist, da Eleyazar ɗan Finehas yana tare da shi, da kuma Lawiyawan nan, wato, Yozabad ɗan Yeshuwa, da Nowadiya ɗan Binnuyi.

34Aka yi lissafi aka auna kome aka tarar yana nan daidai, aka kuma rubuta yawan nauyin a lokacin.

35Sa’an nan sai waɗanda suka dawo daga bauta suka miƙa hadaya ta ƙonawa ga Allah na Isra’ila. Wato, bijimai guda goma sha biyu don Isra’ilawa duka, raguna tasa’in da shida, ’yan raguna saba’in da bakwai, bunsurai kuma guda goma sha biyu. Aka miƙa su hadaya don zunubi. Wannan duka hadaya ta ƙonawa ce ga Ubangiji.

36Suka kuma kai saƙon sarki zuwa ga wakilansa, da kuma gwamnoni na Kewayen Kogin Yuferites waɗanda suka taimaki mutane da kuma gidan Allah.

← Ezra 7 Ezra Ezra 9 →