1Ga lissafin waɗanda suka dawo daga bauta a Babilon, waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwasa zuwa bauta a ƙasar Babilon (sun dawo Urushalima da Yahuda, kowa ya koma garinsu.
2Sun komo tare da Zerubbabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Serahiya, da Re’elaya, da Mordekai, da Bilshan, da Misfar, da Bigwai, da Rehum, da Ba’ana).
3Zuriyar
4ta Shefatiya 372
5ta Ara 775
6ta Fahat-Mowab (ta wurin Yeshuwa da Yowab) 2,812
7ta Elam 1,254
8ta Zattu 945
9ta Zakkai 760
10ta Bani 642
11ta Bebai 623
12ta Azgad 1,222
13ta Adonikam 666
14ta Bigwai 2,056
15ta Adin 454
16ta Ater (ta wurin Hezekiya) 98
17ta Bezai 323
18ta Yora 112
19ta Hashum 223
20ta Gibbar 95.
21Mutanen
22na Netofa 56
23na Anatot 128
24na Azmawet 42
25na Kiriyat Yeyarim,2.25 Dubi Seftuwajin (dubi kuma Neh 7.29); da Ibraniyanci Kiriyat Arim da Kefira Beyerot 743
26na Rama da Geba 621
27na Mikmash 122
28na Betel da Ai 223
29na Nebo 52
30na Magbish 156
31na ɗayan Elam ɗin 1,254
32na Harim 320
33na Lod, da Hadid da Ono 725
34na Yeriko 345
35na Sena’a 3,630.
36Firistoci.
37ta Immer 1,052
38ta Fashhur 1,247
39ta Harim 1,017.
40Lawiyawa.
41Mawaƙa.
42Masu tsaron haikali.
43Ma’aikatan haikali.
44Keros, Siyaha, Fadon,
45Lebana, Hagaba, Akkub,
46Hagab, Shamlai, Hanan,
47Giddel, Gahar, Reyahiya,
48Rezin, Nekoda, Gazzam,
49Uzza, Faseya, Besai,
50Asna, Meyunawa, Nefussiyawa,
51Bakbuk, Hakufa, Harhur,
52Bazlut, Mehida, Harsha,
53Barkos, Sisera, Tema,
54Neziya da Hatifa.
55Zuriyar bayin Solomon.
56Ya’ala, Darkon, Giddel,
57Shefatiya, Hattil,
58Dukan zuriyar ma’aikatan haikali, da kuma bayin Solomon 392.
59Waɗannan mutanen ne suka zo daga garuruwan Tel-Mela, Tel-Harsha, Kerub, Addan da Immer, amma ba su iya nuna ainihin tushensu daga Isra’ila ba.
60’Yan zuriyar
61Daga cikin firistoci kuma,
62Waɗannan sun nemi sunayen iyalansu a cikin littafin da ake rubuta sunayen amma ba su ga sunayensu ba, saboda haka sai aka hana su zama firistoci domin an ɗauka su marasa tsabta ne.
63Gwamna ya umarce su cewa kada su ci wani abinci mai tsarki sai firist ya yi shawara ta wurin Urim da Tummim tukuna.
64Yawan jama’ar duka ya kai mutum 42,360,
65ban da bayinsu maza da mata 7,337; suna kuma da mawaƙa maza da mata 200.
66Suna da dawakai guda 736, alfadarai 245,
67raƙuma 435, da jakuna 6,720.
68Sa’ad da suka isa haikalin Ubangiji a Urushalima, sai waɗansu shugabannin iyalai suka yi bayarwar yardar rai ta gudummawarsu domin sāke gina gidan Allah a wurin da yake.
69Bisa ga ƙarfinsu suka bayar da darik 61,000 na zinariya, da maina 5,000 na azurfa, da rigunan firistoci guda 100.
70Firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da masu aiki a haikali, tare da waɗansu mutane, da dukan sauran Isra’ilawa suka zauna a garuruwansu.