We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

Mai Hadishi 9

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← Mai Hadishi 8 Mai Hadishi Mai Hadishi 10 →

1Sai na yi tunani a kan wannan na kuma gane cewa masu adalci da masu hikima da kuma abubuwan da suke yi suna a hannun Allah ne, amma ba wanda ya san ko ƙauna ko ƙiyayya ce take jiransa.

2Dukansu makomarsu ɗaya ce, masu adalci da masu mugunta, masu kirki da marasa kirki, masu tsabta da marasa tsabta, masu miƙa hadaya da waɗanda ba sa yi.

3Wannan ita ce muguntar da take faruwa a cikin dukan abubuwa a duniya. Ƙaddara ɗaya ce take a kan kowa. Amma zukatan mutane cike suke da mugunta, akwai kuma hauka a zukatansu yayinda suke a raye, bayan haka kuma sai su mutu.

4Duk wanda yake da rai a wannan duniya ta rayayyu, yana sa zuciya, gara rayayyen kare da mataccen zaki!

5Gama rayayyu sun san za su mutu,

6Ƙaunarsu, ƙiyayyarsu,

7Yi tafiyarka, ka ci abincinka da farin ciki, ka sha ruwan inabinka da farin zuciya, gama abin da ka yi duka daidai ne a wurin Allah.

8Kullum ka kasance cikin farin riguna, ka kuma shafe kanka da mai kullum,

9Ka more rayuwa da matarka, wadda kake ƙauna, dukan kwanakin nan marasa amfani da Allah ya ba ka a duniya. Gama wannan ne rabonka a rayuwa da kuma na faman aikinka a duniya.

10Duk abin da hannunka yake yi, ka yi shi da dukan ƙarfinka, gama a cikin kabari in da za ka, babu aiki ko shirye-shirye, ko sani, ko hikima.

11Na kuma ga wani abu a duniya.

12Ban da haka ma, ba wanda ya san sa’ad da lokacin mutuwarsa zai yi.

13Na kuma ga wani misali game da hikima a duniya wanda ya burge ni sosai.

14An yi wani ɗan ƙaramin birni mai mutane kaɗan a ciki. Sai wani babban sarki ya kawo masa yaƙi, ya kafa masa babban sansani.

15A cikin birnin nan kuwa akwai wani mutum matalauci amma mai hikima, ya kuma ceci birnin ta wurin hikimarsa. Amma ba wanda ya tuna da matalaucin nan.

16Sai na ce, “Hikima ta fi ƙarfe ƙarfi.” Amma aka rena hikimar matalaucin, ba a ma jin maganarsa.

17Raɗar mai hikima da aka saurara cikin natsuwa

18Hikima ta fi kayan yaƙi,

← Mai Hadishi 8 Mai Hadishi Mai Hadishi 10 →