1Dawuda ya rera wannan waƙa ga Ubangiji, sa’ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun dukan abokan gābansa, da kuma daga hannun Shawulu.
2Ya ce,
3Allahna shi ne dutsena. A gare shi nake samun kāriya
4“Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo,
5Raƙumar ruwan mutuwa sun kewaye ni;
6Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe ni;
7“A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji;
8Ƙasa ta yi rawa ta kuma girgiza,
9Hayaƙi ya taso daga kafaffen hancinsa;
10Ya buɗe sararin sama, ya sauko ƙasa,
11Ya hau kerubobi, ya tashi sama;
12Ya mai da duhu abin rufuwarsa
13Daga cikin hasken gabansa
14Ubangiji ya yi tsawa daga sararin sama;
15Ya harbe kibiyoyi, ya wartsar da abokan gāba,
16Aka bayyana kwarin teku,
17“Daga sama ya miƙo hannu ya ɗauke ni,
18Ya kuɓutar da ni daga hannun abokin gāba mai iko,
19Suka auka mini cikin ranar masifata,
20Ya fito da ni, ya kai ni wuri mafi fāɗi;
21“Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina;
22Gama na kiyaye hanyoyin Ubangiji;
23Dukan dokokinsa suna a gabana;
24Ba ni da laifi a gabansa
25Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina
26“Ga masu aminci, kakan nuna kanka mai aminci,
27ga masu tsarki, kakan nuna musu tsarki.
28Kakan ceci mai tawali’u,
29Ya Ubangiji kai ne fitilata;
30Da taimakonka zan iya auka wa rundunar sojoji;
31“Ga Allah dai, hanyarsa cikakkiya ce;
32Gama wane ne Allah, in ba Ubangiji ba?
33Allah ne ya ba ni ƙarfi,
34Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa;
35Ya hori hannuwana don yaƙi,
36Ka ba ni garkuwar nasararka;
37Ka fadada hanya a ƙarƙashina
38“Na fafari abokan gābana, na murƙushe su;
39Na hallaka su ƙaƙaf, ba kuwa za su ƙara tashi ba,
40Ka ba ni ƙarfi don yaƙi;
41Ka sa abokan gābana suka juya a guje,
42Suka nemi taimako, amma babu wanda zai cece su,
43Na murƙushe su, suka yi laushi kamar ƙura;
44“Ka kuɓutar da ni daga harin mutanena;
45baƙi kuma su na zuwa don su yi mini fadanci;
46Zukatansu ta karaya;
47“Ubangiji yana a raye! Yabo ta tabbata ga Dutsena!
48Shi ne Allahn da yake rama mini,
49wanda ya kuɓutar da ni daga maƙiyina.
50Saboda haka, zan yabe ka, ya Ubangiji cikin dukan al’ummai;
51“Ya ba wa sarkinsa kyakkyawan nasara;