We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

2 Samaʼila 16

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← 2 Samaʼila 15 2 Samaʼila 2 Samaʼila 17 →

1Sa’ad da Dawuda ya yi ɗan nesa da ƙwanƙolin, sai ga Ziba mai hidimar Mefiboshet, yana jira yă tarye shi. Yana da jerin jakuna da sirdi suna ɗauke da dunƙulen burodi ɗari biyu, da ƙosai busasshen inabi ɗari ɗaya, da kosan ’ya’yan itace ɓaure guda ɗari, da salka ruwan inabi.

2Sarki ya ce wa Ziba, “Me ya sa ka kawo waɗannan?”

3Sai sarki ya ce, “Ina jikar maigidanka?”

4Sai sarki ya ce wa Ziba, “Duk abin da yake na Mefiboshet, ya zama naka.”

5Yayinda Sarki Dawuda ya kusato Bahurim, sai ga wani mutumin dangin Shawulu ya fito daga can, sunansa Shimeyi ɗan Gera. Ya fito yana ta la’anta yayinda yake fitowa.

6Ya jajjefi Dawuda da dukan fadawan sarki da duwatsu, ko da yake sojoji da masu gadin sarki na musamman suna kewaye da sarki dama da hagu.

7Yayinda yake la’antar, Shimeyi ya ce, “Tafi daga nan, tafi daga nan, mai kisankai, mutumin banza kawai!

8Ubangiji ya kama ka saboda alhakin jinin gidan Shawulu, wanda kake sarauta a maimakonsa. Ubangiji ya ba da masarautar ga ɗanka Absalom. Hallaka ta zo maka domin kai mai kisankai ne!”

9Sai Abishai ɗan Zeruhiya ya ce wa sarki, “Ranka yă daɗe, don me wannan mataccen kare yake la’antarka? Bari in je in datse kansa.”

10Amma sarki ya ce, “Ba ruwana da ku, ku ’ya’yan Zeruhiya. Idan yana la’ana ne domin Ubangiji ya ce masa, ‘La’anci Dawuda,’ wa zai ce, ‘Don me kake haka?’ ”

11Sa’an nan Dawuda ya ce wa Abishai da dukan fadawansa, “Ɗana, na cikina, yana ƙoƙari yă kashe ni. Balle wannan mutumin Benyamin! Ku ƙyale shi, yă yi ta zargi, Ubangiji ne ya ce masa yă yi haka.

12Mai yiwuwa Ubangiji yă ga azabata, yă sāka mini da alheri saboda la’anar da nake sha a yau.”

13Saboda haka Dawuda da mutanensa suka ci gaba da tafiyarsu yayinda Shimeyi yana tafiya ɗaura da shi a gefen tudu, yana zagi, yana jifansa da duwatsu, yana tayar masa da ƙura.

14Sarki da dukan mutanen da suke tare da shi suka isa masauƙinsu a gajiye. A can fa ya huta.

15Ana cikin haka, Absalom da dukan Isra’ila suka iso Urushalima, Ahitofel kuwa yana tare da shi.

16Sai Hushai mutumin Arkitawa, abokin Dawuda ya je wurin Absalom ya ce masa, “Ran sarki yă daɗe! Ran sarki yă daɗe!”

17Absalom ya ce wa Hushai, “Ƙaunar da kake nuna wa abokinka ke nan? Me ya sa ba ka tafi tare da abokinka ba?”

18Hushai ya ce wa Absalom, “A’a, ai, wanda Ubangiji ya zaɓa ta wurin waɗannan mutane, da kuma ta wurin dukan mutane Isra’ila, shi zan zama nasa, zan kuma kasance tare da shi.

19Ban da haka ma, wane ne zan bauta wa? Ashe, ba ɗan ne zan bauta wa ba? Kamar dai yadda na bauta wa mahaifinka, haka zan bauta maka.”

20Absalom ya ce wa Ahitofel, “Ba mu shawararka. Me za mu yi?”

21Ahitofel ya ce wa Absalom, “Je ka kwana da ƙwarƙwaran mahaifinka waɗanda ya bari su lura da fada. Ta haka dukan Isra’ila za su ji cewa ka mai da kanka abin wari a hancin mahaifinka, dukan hannuwan waɗanda suke tare da kai kuwa za su sami ƙarfi.”

22Saboda haka suka kafa wa Absalom tenti a bisa rufin ɗaki, a can ya kwana da ƙwarƙwaran mahaifinsa a gaban dukan Isra’ila.

23To, a kwanakin nan shawarar da Ahitofel yakan bayar takan zama kamar wadda aka nemi daga Allah ne. Haka Dawuda da Absalom duk suke ɗaukan dukan shawarar Ahitofel.

← 2 Samaʼila 15 2 Samaʼila 2 Samaʼila 17 →