We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

2 Tarihi 17

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← 2 Tarihi 16 2 Tarihi 2 Tarihi 18 →

1Yehoshafat ɗansa ya gāje shi a matsayin sarki ya kuma kahu sosai gāba da Isra’ila.

2Ya kafa mayaƙa a dukan biranen katangar Yahuda, ya kuma sa runduna a Yahuda da kuma a garuruwan Efraim da mahaifinsa Asa ya ci da yaƙi.

3Ubangiji kuwa yana tare da Yehoshafat domin a shekarunsa na farko-farko ya yi tafiya a hanyoyin da kakansa Dawuda ya bi. Bai nemi shawarar Ba’al ba

4amma ya nemi Allah na kakansa ya kuma bi umarnansa a maimakon ayyukan da Isra’ila ke yi.

5Ubangiji ya kafa mulkin a ƙarƙashin ikonsa; dukan Yahuda kuwa suka kawo kyautai wa Yehoshafat, ta haka ya yi arziki sosai da kuma girma.

6Zuciyarsa ta duƙufa ga hanyoyin Ubangiji, bugu da ƙari, ya kawar masujadan kan tudu da ginshiƙan Ashera daga Yahuda.

7A shekara ta uku ta mulkinsa, ya aiki ma’aikatansa Ben-Hayil, Obadiya, Zakariya, Netanel da Mikahiya su yi koyarwa a garuruwan Yahuda.

8Tare da su akwai waɗansu Lawiyawa, Shemahiya, Netaniya, Zebadiya, Asahel, Shemiramot, Yehonatan, Adoniya, Tobiya da Tob Adoniya, da kuma firistoci Elishama da Yehoram.

9Suka yi koyarwa a dukan Yahuda, suna ɗauke da Littafin Dokar Ubangiji tare da su; suka tafi ko’ina a dukan garuruwan Yahuda suka koyar da mutane.

10Tsoron Ubangiji ya kama dukan masarautun ƙasashen da suke kewaye da Yahuda, har ba su yi yaƙi da Yehoshafat ba.

11Waɗansu Filistiyawa suka kawo wa Yehoshafat kyautai da azurfa a matsayin haraji, Larabawa kuwa suka kawo masa garkuna, raguna dubu bakwai da ɗari bakwai da kuma awaki dubu bakwai da ɗari bakwai.

12Yehoshafat ya yi ta ƙaruwa a ƙarfi; ya gina katanga da biranen ajiya a Yahuda

13da kuma tanade-tanade masu yawa a garuruwan Yahuda. Ya kuma ajiye gogaggu mayaƙa a Urushalima.

14Ɗaukar da aka yi musu bisa ga iyalai yana kamar haka.

15biye da shi, Yehohanan shi ne shugaba, yana da sojoji 280,000;

16biye da shi, Amasiya ɗan Zikri, wanda ya ba da kansa da yardar rai don hidimar Ubangiji, yana da sojoji 200,000.

17Daga Benyamin,

18biye da shi, Yehozabad, yana da sojoji 18,000 shiryayyu don yaƙi.

19Waɗannan su ne suka yi wa sarki hidima, ban da waɗanda aka sa a biranen katanga ko’ina a Yahuda.

← 2 Tarihi 16 2 Tarihi 2 Tarihi 18 →