We Believe JesusFé, Esperança e Nova Vida

1 Samaʼila 3

Biblica® Buɗaɗɗen Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™ · hauçá

← 1 Samaʼila 2 1 Samaʼila 1 Samaʼila 4 →

1Yaron nan Sama’ila ya yi hidima a gaban Ubangiji a ƙarƙashin Eli. A waɗannan kwanaki kuwa jin magana daga wurin Ubangiji ba safai ba, babu kuma wahayi da yawa.

2Wata rana da dare Eli da idanunsa sun kusa makancewa har ba ya iya gani sosai yana kwance a inda ya saba.

3Fitilar Allah kuwa tana ci, ba tă mutu ba tukuna, Sama’ila kuma na kwance a haikali na Ubangiji inda akwai akwatin Allah.

4Sai Ubangiji ya kira Sama’ila.

5Sai ya ruga wajen Eli ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.”

6Ubangiji ya sāke kiransa ya ce, “Sama’ila!” Sama’ila ya tashi kuma ya je wurin Eli ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.”

7Sama’ila dai bai riga ya san Ubangiji ba tukuna. Ba a kuma taɓa bayyana maganar Ubangiji a gare shi ba tukuna ba.

8Ubangiji ya kira Sama’ila sau na uku, Sama’ila kuma ya tashi ya tafi wurin Eli, “Ga ni, gama ka kira ni.”

9Saboda haka, Eli ya gaya wa Sama’ila cewa, “Je ka kwanta, in kuma ya kira ka, ka ce masa, ‘Ya Ubangiji ka yi magana gama bawanka yana saurara.’ ” Sama’ila ya koma ya kwanta a wurin kwanciyarsa.

10Ubangiji kuma ya zo ya tsaya a wurin, yana kira ya ce, “Sama’ila, Sama’ila!” Kamar yadda ya kira a lokutan baya.

11Ubangiji ya ce wa Sama’ila, “Duba ina dab da yin wani abu a Isra’ila da zai sa kunne kowa da yake ji, yă ji tsoro.

12A ranar zan cika dukan maganar da na yi game da Eli da iyalinsa, daga farko har ƙarshe.

13Gama na gaya masa zan hukunta gidansa har abada saboda zunubin da yake sane da shi; ’ya’yansa sun wulaƙantar da kansu, shi kuma bai tsawata musu ba.

14Saboda haka na rantse a kan gidan Eli, ‘Ba za a taɓa shafe laifin gidan Eli da hadaya ko baiko ba.’ ”

15Sama’ila kuwa ya kwanta har safe, sa’an nan ya buɗe ƙofofin gidan Ubangiji. Ya ji tsoro yă gaya wa Eli wahayin,

16amma Eli ya kira shi ya ce, “Sama’ila, ɗana.”

17Eli ya ce, mene ne ya ce maka? Kada ka ɓoye mini. Allah ya yi da kai har ma fiye in ka ɓoye mini kome da ya ce maka.

18Don haka sai Sama’ila ya gaya masa kome bai ɓoye masa kome ba. Sa’an nan Eli ya ce, “Shi ne Ubangiji bari yă yi abin da ya yi kyau a gare shi.”

19Ubangiji kuwa yana tare da Sama’ila har girmansa bai kuma bar ko ɗaya daga maganarsa ta kāsa cika ba.

20Dukan Isra’ila daga Dan har Beyersheba suka shaida amincin Sama’ila annabi ne na Ubangiji.

21Ubangiji kuwa ya dinga bayyana a Shilo, a nan ya bayyana kansa ga Sama’ila ta wurin maganarsa.

← 1 Samaʼila 2 1 Samaʼila 1 Samaʼila 4 →