1Sai Sarki Solomon ya yi mulki a bisa dukan Isra’ila.
2Waɗannan su ne manyan shugabanninsa.
3Elihoref da Ahiya, ’ya’yan Shisha maza, su ne marubuta.
4Benahiya ɗan Yehohiyada, shi ne shugaban mayaƙa.
5Azariya ɗan Natan, shi ne mai lura da shugabannin yanki.
6Ahishar, shi ne sarkin fada.
7Solomon yana da gwamnoni yankuna goma sha biyu a bisa dukan Isra’ila, waɗanda suke tanaji abinci domin sarki da kuma gidan sarauta. Kowanne yakan tanada abinci na wata ɗaya a shekara.
8Ga sunayensu,
9Ben-Deker, shi ne a Makaz, Sha’albim, Bet-Shemesh da Elon Bet-Hanan;
10Ben-Hesed, shi ne a Arubbot (Soko da dukan ƙasar Hefer);
11Ben-Abinadab, shi ne a Nafot Dor (ya auri Tafat ’yar Solomon);
12Ba’ana ɗan Ahilud, shi ne a Ta’anak da Megiddo, da kuma dukan Bet-Sheyan biye da Zaretan ƙasa da Yezireyel, daga Bet-Sheyan zuwa Abel-Mehola a ƙetaren Yokmeyam;
13Ben-Geber, shi ne a Ramot Gileyad (Mazaunan Yayir ɗan Manasse a Gileyad suna a ƙarƙashinsa, haka ma yankin Argob a Bashan tare da manyan biranen sittin masu katanga da suke da ƙyamare na tagulla);
14Ahinadab ɗan Iddo, shi ne a Mahanayim;
15Ahimawaz, shi ne a Naftali (ya auri Basemat ’yar Solomon);
16Ba’ana ɗan Hushai, shi ne a Asher da Bayelot;
17Yehoshafat ɗan Faruwa, shi ne a Issakar;
18Shimeyi ɗan Ela, shi ne a Benyamin;
19Geber ɗan Uri, shi ne a Gileyad (ƙasar Sihon sarkin Amoriyawa da kuma Og sarkin Bashan). Shi ne kaɗai gwamna a bisa yankin.
20Mutanen Yahuda da na Isra’ila sun yi yawa sai ka ce yashi a bakin teku. Suka ci, suka sha, suka kuma yi farin ciki.
21Solomon kuwa ya yi mulki a bisa dukan masarautai daga Kogi4.21 Wato, Yuferites; haka ma a aya 24. zuwa ƙasar Filistiyawa, har zuwa iyakar Masar. Waɗannan ƙasashe sun yi ta kawo haraji, suka kuma zama bayin Solomon dukan kwanakin ransa.
22Tanajin Solomon na kowace rana su ne, garwa talatin na garin abinci,
23shanun da aka yi kiwo a gida guda goma, shanu ashirin da suka ƙoshi daga kiwo, tumaki da awaki ɗari; ban da ƙishimai, bareyi, batsiyoyi, da kaji masu ƙiba.
24Gama ya yi mulki a bisa dukan masarautai yamma da Kogi, daga Tifsa zuwa Gaza, aka kuwa sami zaman lafiya a kowane gefe.
25A kwanakin da Solomon yake raye, Yahuda da Isra’ila, daga Dan zuwa Beyersheba, sun zauna lafiya, kowane mutum ya zauna a ƙarƙashin itacen inabi da na ɓaurensa.
26Solomon yana da rumfunan dawakai masu jan kekunan yaƙi, dubu huɗu,4.26 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na Seftuwajin (dubi kuma 2Tar 9.25); Ibraniyanci na da arba’in da kuma dawakai dubu goma sha biyu4.26 Ko kuwa masu hawa
27Shugabannin yankuna, kowanne a watansa yakan yi tanajin abinci domin Sarki Solomon da kuma duk wanda ya zo teburin sarki. Sun tabbatar ba a rasa kome ba.
28Kowa a cikinsu, bisa ga lokacin da aka ba shi, yakan kai hatsin sha’ir da ciyawa domin dawakan-kekunan yaƙi, da sauran dawakai a inda aka ajiye su.
29Allah ya ba Solomon hikima da hangen nesa mai girma, da kuma fāɗin fahimta marar iyaka, kamar yashi a bakin teku.
30Hikimar Solomon ta fi hikimar mutanen Gabas, ta kuma fi dukan hikimar Masar girma.
31Ya fi kowane mutum hikima, har da Etan dangin Ezra ma. Yana da hikima fiye da Heman, Kalkol da Darda, ’ya’yan Mahol maza. Sunansa ya bazu ko’ina a ƙasashen da suke kewaye.
32Ya yi karin magana dubu uku. Waƙoƙinsa kuwa sun kai dubu ɗaya da biyar.
33Ya yi magana a kan rayuwar itatuwa, daga al’ul na Lebanon zuwa hizzob da yake girma a bangaye. Ya kuma yi koyarwa game da dabbobi, da tsuntsaye, da abubuwa masu rarrafe, da kuma kifi.
34Mutane suka yi ta zuwa daga ƙasashe dabam-dabam don su ji hikimar Solomon. Sarakuna daga ko’ina a duniya, sun ji labarin hikimarsa, suka kuma aika da mutane don su ji shi.