1Suka fa kawo akwatin alkawarin Allah, suka sa a cikin tentin da Dawuda ya kafa dominsa, suka kuma miƙa hadayun ƙonawa da hadayu na salama a gaban Allah.
2Bayan Dawuda ya gama miƙa hadayu na ƙonawa da hadayu na salama, sai ya albarkaci mutane a cikin sunan Ubangiji.
3Sa’an nan ya ba da dunƙulen burodi da wainar dabino da kuma kauɗar zabibi ga kowane mutumin Isra’ila namiji da ta mace.
4Ya sa Lawiyawa su yi hidima a gaban akwatin alkawarin Ubangiji, su ɗaukaka, su gode, su kuma yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila.
5Asaf shi ne babba, sai Zakariya na biye, sa’an nan Ya’aziyel, Shemiramot, Yehiyel, Mattitiya, Eliyab, Benahiya, Obed-Edom da Yehiyel. Su ne za su kaɗa molaye, da garayu, Asaf kuwa zai buga ganguna,
6Benahiya da Yahaziyel firistoci za su busa ƙahoni kullum a gaban akwatin alkawarin Allah.
7A wannan rana, da farko, Dawuda ya sa Asaf da ’yan’uwansa su rera wannan zabura ta yabo ga Ubangiji.
8Ku yi godiya ga Ubangiji, ku yi shelar sunansa;
9Ku rera gare shi, ku rera yabo gare shi;
10Ku ɗaukaka a cikin sunansa mai tsarki
11Ku dogara ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa;
12Ku tuna ayyukan banmamakin da ya aikata,
13Ya ku zuriyar Isra’ila bayinsa,
14Shi ne Ubangiji Allahnmu;
15Yakan tuna da alkawarinsa har abada,
16alkawarin da ya yi wa Ibrahim
17Ya tabbatar da shi ga Yaƙub kamar ƙa’ida,
18“Gare ka zan ba da ƙasar Kan’ana
19Sa’ad da suke kima,
20suka yi ta yawo daga al’umma zuwa al’umma,
21Bai bar wani ya zalunce su ba;
22“Kada ku taɓa shafaffuna;
23Ku rera ga Ubangiji, ku duniya duka;
24Ku furta ɗaukakarsa a cikin al’ummai,
25Gama Ubangiji mai girma ne ya kuma cancanci yabo;
26Gama dukan allolin al’ummai gumaka ne,
27Daraja da ɗaukaka suna a gabansa;
28Ku yabi Ubangiji, ku iyalan al’ummai,
29ku ba wa Ubangiji ɗaukakar da ta dace da sunansa.
30Ku yi rawar jiki a gabansa, ya ku duniya duka!
31Bari sammai su yi farin ciki, bari duniya tă yi murna;
32Bari teku da kome da yake cikinsa su yi ruri;
33Sa’an nan itatuwan jeji za su rera,
34Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne;
35Ku yi kuka, ku ce, “Cece mu, ya Allah Mai Cetonmu;
36Yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila,
37Dawuda ya bar Asaf da ’yan’uwansa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji don su yi hidima a can kullum, bisa ga tsari na kowace rana.
38Ya kuma bar Obed-Edom da ’yan’uwansa sittin da takwas don su yi hidima tare. Obed-Edom ɗan Yedutun da Hosa kuma, su ne matsaran ƙofofi.
39Dawuda ya bar Zadok firist da ’yan’uwansa firistoci a gaban tabanakul na Ubangiji a tudun da yake a Gibeyon
40don su miƙa hadayun ƙonawa ga Ubangiji a kan bagaden hadaya ta ƙonawa kullum, da safe da kuma yamma, bisa ga kome da yake a rubutacce a cikin Dokar Ubangiji, da ya ba wa Isra’ila.
41Tare da su akwai Heman da Yedutun da sauran waɗannan zaɓaɓɓun da aka rubuta sunansu don yin godiya ga Ubangiji, “gama ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”
42Heman da Yedutun su ne da hakkin busa ƙahoni da kaɗa kuge da sauran kayan bushe-bushe da na kaɗe-kaɗe, waɗanda ake amfani da su lokacin da ake rera waƙoƙi masu tsarki. ’Ya’yan Yedutun maza, su aka ba wa aikin tsaron ƙofa.
43Sa’an nan dukan mutanen suka tashi, kowa ya koma gidansa, Dawuda ya koma gida yă sa wa iyalinsa albarka.